23 Yuli 2019 - 04:32
Najeriya: ​An Sace 'Yan Kasar Turkiya Hudu A Jihar Kwara

Rundunar 'yan sandan Najeriya ta tabbatar da sace 'yan kasar Turkiyya hudu a Arewa Ta Tsakiya a kasar.

(ABNA24.com) Rundunar 'yan sandan Najeriya ta tabbatar da sace 'yan kasar Turkiyya hudu a Arewa Ta Tsakiya a kasar.

Kamfanin dillancin labaran Reuteus ya nakalto kakakin 'yan sandar jihar Kwara Okasanmi Ajayi na cewa wasu 'yan bindiga sun yi awan gaba da 'yan kasar Turkiya 4 a kauyen Gbale na yankin Edu dake cikin jihar.

Sanarwar ta kara da cewa mutane hudun da aka yi garkuwa da su ,ma'aikatan wani kamfani ne na gine-gine kuma an sace su ne a wata mashaya.

'Yan sandan sun bayyana cewa suna kokari wajen ganin an cewa ceto wadanda aka yi garkuwa da su.

Sai dai babu wata kungiya da ta dauki alhakin yin garkuwa da ma'aikatan.

Ko a makon da ya gabata ma, sai da 'yan fashi a kan teku suka kai hari ga wani jirgin daukar kaya a gabar tekun Najeriya inda suka yi garkuwa da matukan jirgi 10 'yan kasar Turkiyya. Su ma wadannan babu labarinsu.

Matsalar garkuwa da mutane a Najeriya ta zamo ruwan dare inda masu garkuwa da mutane suka fi mayar da hankali wajen garkuwa da masu hannu da shuni a wani lokacin ma har baki 'yan kasar waje domin neman kudaden fansa.

Duk da irin kokarin da gwamnati ta ce tana yi, har yanzu an kasa magance wannan matsalar.




/129